Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Haihuwar Annabi Isa ( As) ya nuna karfin kudurar Ubangiji da kuma matsayin sayyadatuna Maryam mahaifiyar Annabi Isa (As) da kuma girman matsayin da mace take da shi a addinan da aka saukar daga sama, idan aka tuna lokacin da Mala’ika ya zo mata yace: “ ya maryam hakika Allah ya tsarkakeki kuma ya zabe ki daga cikin matan duniya.
Yace yin bukin tunawa da zagayowar wannan rana wata damace na karrama sayyidatuna maryam (As) kuma lokaci ne na tunawa da koyi da kyawawan halaye na Annabi Isa As, da kuma fada da zalunci da yayi da cusa fata na gari ga raunana domin samun makoma ta gari .
342/